Dandume Reporters
Ingantattun Labarai Ba Tare Da Cin Mutuncin Kowa Ba Shine Manufar Wannan Feji.
Tsohon shugaban riko na karamar hukumar Ɗandume Alh Haruna Ja Abdullahi ya rasu
Allah mai kowa mai komai ya yi wa tsohon shugaban riko na karamar hukumar Ɗandume Alh Haruna Ja Abdullahi rasuwa sak**akon gajeruwar jinya.
Muna rokon Allah Ya ji kansa Ya gafarta amin
Majalisar jihar Katsina tayi wata bita ta kwanaki kan matsalar tsaro data addabi jahar, k**ar yadda tsohon kakakin majalisar Rt. Hon Aliyu Sabi'u Muduru ya wallafa a shafinsa na facebook. Allah ya sa bitar ta amfanar da al'ummar Jahar Katsina musamman kan abinda akayi bitar domin sa Amen.
Daga Lawal Hudu Dandume
A karɓa da haƙuri...
Tsananin kaiwa Number 9 a munafurci ne wani azzalumi yace maka wai laifukanmu ne ya hanamu zaman lafiya kana ya kawo bala'in ta'addancin da ake mana...
Ba wai kuma ina nufin laifi ba zai zama fitina ba, a'a amma dai tsananin ƙin Allah ne wani wanda lokacin gwamnatin baya bai san ana laifin ba sai yanzu don ya kai almuri yace wai ai laifin mune...
Akwai ƙasashen duniya da duk wani laifi da kasan anayi a Nigeria to can an ninkashi (saurari wa'azizzikan Sheikh Bashir Ɗanfili Sokoto). Misali akwai ƙasashen da sun halarta auren jinsi da zina a fili da shan giya da rushe masallatai ma, kai da sauran nau'ikan laifukan da ba don Allah yasa munzo a zamanin fiyayyen halitta ba, da yanzu wani zancen ake, amma waɗannan ƙasashe sune kan gaba a zaman lafiya, saboda adalcin shuwagabanninsu.
Ya k**ata mu sani cewa komin yadda kafirci yake yakan zama cikin salama inda adalci, akasin haka kuma kan faru da Musulunci ko shakka babu..
Ba wani ɗan iska a Nigeria da zaice wai laifinmu yasa ƴan ta'adda ke kashemu malam, Allah ya jarabcemu da asalin azzaluman shuwagabanni ne kawai a sama kana ya jarabcemu da azzaluman malamai da a bakinsu kaɗai Allah yake...
Kuma ai ya k**ata mu sani shin su laifukan da ake cewa daga 2015 zuwa yanzu ne aka fara su don haka sai yanzu hukuncin yazo?
Allahumma dammirhum tadmira.🙏
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun 😭
Allah yayiwa mahaifin Alh Abubakar Salisu Asas rasuwa.
Alh Abubakar Asas shine dan takarar kujerar majalisar tarayya da zai wakilci kananan hukumomin Funtua da Dandume a zaben 2023 karkashin jam'iyar PDP.
Muna addu'a Allah gafartawa mahaifin nasa ya sa aljanna makomarsa Amen.
Innalillahi wainna ilaihi rajiun 😭
Yan ta'adda sun kashe DCP Aminu Umar area commander na dutsimma da yammacin yau talata 5/7/2022.
An ruwaito cewa barayin sunyi musu kwanton bauna ne, kuma s**a halaka shugaban yan sandan
Muna Addu'ar Allah ya gafarta masa ya kyautata makwancinsa Amen
Sabon Alkalin Alkalan Nigeria Kenan, Justice Olukayode Ariwoola.
Dan Karamar Hukumar Dandume Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa A Jam'iyyar APP.
MU NA NAN A APC...
Daga Lawal Hudu Dandume.
Kasan wani baida gadonka amma yana da gadon maganar ka, cece-kuce yayi yawa akan batun wai Baba Hon Haruna Goma ɗan majalisar mu mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗandume karo na biyu kuma shugaban kwamitin muhallin jihar Katsina ya bar Jam'iyyar APC...
Wannan labari ne mara tushe kuma shaci faɗi da wasu waɗanda suke ganin in sune a matsayin shi to haka zasuyi, niko nasan in har Baba ya bar APC to Insha Allah bana tunanin zan wuce mutum goma na farko da zasu fara sani....
Koda ma mukayi magana da Baba Hon Haruna Goma sai ya kashe mun jiki da cewa " Karka manta fa munyi takara a 2015 mukayi nasara, muka nemi tazarce 2019 mukayi nasara, muka ɗaga hannun Alh Yahaya Nuhu Mahuta shima yayi nasara, muka nemi kujerar reps Allah ya bawa waninmu, to kenan in muka bar Jam'iyyar me muke nufi kenan? Shin Ubangijin dake badawa a APC kenan bashi bane a sauran jam'iyyun? Kenan mun munanawa Allah zato cewa sai a wani wuri zai bamu, ba zamuyi haka ba" Inji Baba....
Muna nan daram a APC damu aka ƙirƙireta kuma asalima nina fara cin gajiyarta a duk faɗin ƙaramar hukumar Ɗandume don kuwa ni na fara cin zaɓen fidda gwani a cikinta gaba ɗaya...
Ba kuma zamu zama irin wasu da s**a bar tasu jam'iyyar s**a dawo wata ba saboda rasa mulki cikin yan satittika ba k**ar yadda ya faru a baya..
"Sai dai ba dalilin da baka nememu a hidimarka ba mu shiga ko mu tura yaranmu su shiga wannan kam ba dalili"...
"Kuma ma a halin da muke ciki ya k**ata ne duk mai takara a APC ya himmatu wurin neman hanyar nasarar jam'iyyar ba wai cin zarafin wanda kayi takara tare dasu ba"..
"Akwai matakai da yawa da zamu taimaki APC a matsayinta na jam'iyyar mu wanda yasha banban da irin taimakon da ɗan takara kuma zai iya samu, don munyi gogewar rarrabe su a ma'auni na siyasa".. Inji Baba..
"Duk bamu san me Allah zaiyi gobe ba amma dai maganar barin APC ba gaskiya bane kuma muna cikinta kuma muna tare da waɗanda s**a ga cewa muna da muhimmiyar rawa da gudummawar da zamu basu ba cin mutumci ko cin zarafi ko habaici ko yafice ko muzgune b***e kuma zagi da ƙazafi"...
Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairi ya kuma ƙara dauwamar mana da zaman lafiya a dukkan ƙasarmu da sauran ƙasashen Musulmi Amen.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina ya sayi fom ɗin takarar gwamna
Me fatan ku gareshi?
Sanatan Katsina Ta Arewa Ahmad Babba Kaita, Ya Fice Daga Jamiyyar APC Zuwa PDP.
Meye Fatanku Gareshi?
Mallam Ya'u Nowa Ahmad Ya Lashe Zaben Karamar Hukumar Dandume A Zaben Jiya Litinin.
Munawa Malam Murna Da Addu'ar Allah Taya Riƙo.
Ya kuke kallon al'adar kidan Gwauro??
Marhabun bi shahril azim.
Allah muna rokonka ka karbi dukkan ibadunmu ka kuma saka mu a cikin bayinka yantattu a cikin wannan wata mai albarka, Allah kuma muna rokonka albarkar wannan wata ka kawo mana karshen dukkan wata fitina data addabi kasar mu dama dukkan kasashen Musulmin Duniya Amen..
Ramadan kareem.
Ba cikin kankanin lokaci matasan karamar hukumar Dandume zasu manta da Kabiru Jagoos ba.
Muna kara addu'a Allah ya jaddada masa rahama.
Ya zuwa yanzu dai yan takarar Kujerar Dan majalisar jaha ta karamar hukumar Dandume biyu ne s**a bayyana daga jamiyyar PDP.
Daga ciki akwai tsohon dan majalisar wanda ya rike kujerar daga shekarar 2011 zuwa 2015, kafin Hon Haruna Goma ya kada shi wato Hon Alh Isyaku Lawal.
Sannan akwai Hon Hamisu Abdullahi Garkuwa wanda dane a wurin tsohon ma'ajin jamiyyar PDP ta jihar Katsina, lokacin gwamnatin shema.
Tunda dai ba'a zo fagen da talaka zai tada jijiyar wuya ba, (har sai exco sun gama nasu) amma duk da haka wa kake wa fatan alkhairi?
Tsohon shugaban karamar hukumar faskarin jahar Katsina, tsohon dan majalisar taraiya mai Wakiltar kankara faskari sabua, tsohon Kwamishinan ilmin jihar Katsina kana tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua Alhaji Shehu Inuwa Imam ya sayi foam din tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a jamiyyar PDP.
Wane fata kuke masa?
Alamu sun nuna cewa Injiniya Muaz Magaji ya koma PDP yayin da aka hango shi rike da tutar jam'iyyar a wurin taron kaddamar da takarar Alh Atiku Abubakar
Alamu na nuna cewa gwagwarmayar neman kujerar gwamnan jihar Katsina a APC za'a fafata ne tsakanin sakataren gwamnatin jihar Dr Mustapha Muhd Inuwa da kuma shugaban bankin bada lamuni Arc Ahmad Musa dangiwa.
Wa kuke fata?
Jiya talata 15/03/2022 sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Mustapha muhammad inuwa ya kaddamar da kudurinsa na takarar gwamnan jihar Katsina.
Taron ya gudana a sakateriyar jamiyyar APC ta jihar Katsina dake a birnin na katsina, taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati k**ar yan majalisun taraiya dana jaha da yan takarar chiyamomi na jihar ta katsina.
Shugaban jam'iyyar APC Alh Sani Ali Daura da mataimakinsa Alh Bala Abubakar Musawa sun gabatar da muhimman jawabai yayin taron.
Daga karshe shima dan takarar ya gabatar da nasa jawabin cikin jawabinsa yake cewa "duk wani dan jamiyyar APC dake jihar katsina ba wanda bai nemi taimako a wurin mu ba kuma mun taimaka masa, don haka ne muma yanzu muke so ayi mana"
To muna muna addu'a Allah ya zaba mana dukkan abinda zai zama alkhairi ga jihar Katsina dama kasa baki daya.
Matashin dake tattaki daga Abuja zuwa Lagos don rokon tinubu ya fito takarar shugaban kasa ya isa garin okene da safiyar nan.
Meye fatanku gareshi?
Daga Daily News Hausa.
ZAƁEN 2023 | Babban kuskuren da Jam'iyyar APC za ta tafka mafi muni shi ne ta yi gangancin baiwa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu tikitin takarar Shugaban kasa domin alƙalumma sun nuna cewa bazai taɓa samun karɓuwa da goyan bayan mutanen yankin Arewa dana kudu maso kudancin Najeriya ba.
Musanman idan mu kayi laka'ari da yawan shekarunsa da rashin lafiyar da yake fama da ita da nuna ƙabilacin wariyar yanki da kuma tasgaron da za'a samu wajen zaɓo masa mataimaki daga yankin Arewacin Najeriya.
Wannan zai sanya idan har Jam'iyyar tai kuskuren bashi takara 2023 tabbas ba lalle bane Jam'iyyar ta iya sake cin zaɓe.
Cewar matashin Ɗan gwagwarmaya Comr Nura Siniya.
Ya kuke kallon wannan batu?
Daga Shafin
BBC Hausa,
Gwamnatin Nigeria ta amince zata mika DCP Abba kyari ga kasar Amurka.
Tun dai shekarar data gabata ne akayi zargin dan sandan da alaka da babban dan damfara hushpuppi, kana kuma cikin wannan sabuwar shakara aka kara k**a dan sandan dumu-dumu da harkallar miyagun kwayoyi.
Allah shine mafi sani akan lamarin DCP Abba kyari, mu dai namu ido da kuma addu'ar Allah bawa mai gaskiya gaskiyarsa.
Sabuwar Jam'iyyar Madugun Tafiyar Kwankwasiyya Kenan, Alhaji Dr Rabi'u Musa Kwankwaso Mai Suna "New Nigerian Peoples Party".
Meye Fatanku Ga Madugu?
The battle of the titans!!
Dangoma/Dandutse.
Allah bamu dukkan wanda zai zama alkhairi.
Kasar Rasha ta fito da makaminta mafi muni mai suna 'SATAN 2', Fito da makamin gargadi ne ga duk wata kasa da ta saka musu baki a fadansu da kasar Ukraniya.
Me zaku ce?🤔
SHUGABAN KASAR UKRAIN YA SHIRYA WA BARIN DUNIYA
Daga Datti Assalafiy
Shugaban Kasar Ukraine Mr Volodymyr Zalenskyy ya fito fagrn yaki cikin shigar sojojin kundunbala, kuma yayi kira ga duk wani 'dan Kasar Ukraine yazo ya karbi kowani irin makamin yaki domin su dakile Kasar Russia
Da yake yaki ne tsakanin kasashen da ba Musulmai ba, amma wannan matakin da Shugaban Kasar Ukraine ya dauka ya burgeni, wannan shine shugaba mai kishin al'umma
Haka ake son shugaba wanda zai iya wucewa gaba a fagen yaki, ba shugabanni matsorata irin namu ba wadanda mota ma basa iya hawa b***e su fita fagen yaki
Shafin Arewa Intelligence zai kawo bayani nan gaba akan abinda ya haddasa rikicin Russia da Ukraine wanda zai iya shafar duk duniya ya kuma haddasa karayar tattalin arzikin duniya
Muna rokon Allah Ya sa fitinar ta kare a kansu
Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa ga senator Abdullahi Adamu a matsayin APC National Chairman party.
To kenan ina Makomar
Alh Abdulaziz Abubakar Yari
Alh ALI MODU SHERIFF
Alh Umaru Tanko Almakura
Kuma an tabbatar da cewa shi senator Abdullahi Adamu baifi ko sati biyu da baiyana niyyarsa ta neman Kujerar ba.
Meye fatanku ga Jam'iyyar APC?
Allahu Akbar.
Rasuwar Sidi Garba Da Yammacin Yau Litinin 21/02/2022, Ta Girgiza Al'ummar Garin Dandume Da Kewaye, Muna Addu'a Allah Ya Gafarta Masa Yasa Aljanna Makomarsa Ya kuma Bawa Yan'uwa Da Iyalinsa Da Kuma Al'ummar Dandume Hakurin Rashinsa.
Jiya Lahadi 20/2/2022..
Jam'iyyar PDP ta gabatar da gagarumin taron bada tutoci da yan takarkarinta a karamar hukumar DANDUME, Taron ya samu halartar manyan jigajigan jam'iyyar ta PDP na jaha dana karamar hukumar ta dandume irinsu..
Alh Kabir Mai Wada Daudawa
Alh Abdulaziz Ahmad Tijjani (Bega)
Alh Garba Na'aja
Alh Mustapha Abdulkadir
Alh Lawal Isyaku Tumburkai
Hon Bishir Yusuf Mai kwano
Hon Hamisu Abdullahi Garkuwa
Da Kuma Dubban Magoya Bayan Jam'iyyar Ta PDP.
Muna Addu'ar Allah Ya Zaba Mana Dukkan Abinda Zai Zama Alkhairi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Katsina
Shahura
Katsina
Domin samun Labarai tare da ruhotanni akan al'amuran da s**a shafi tsaro a Nijeriya tare da makwabta
No 140 Mani House, Yahaya Madaki Way Kofar Ƙaura New Lay-out Katsina
Katsina
Hausa da Al'adu is a platform that is being operated by CONTENT AND CLIPS Media Services Limited, a
Katsina
Katsina Digest is a news outlet that serves as a Gateway To The Home Of Hospitality in Nigeria 🇳🇬
Yahaya Madaki Way
Katsina, 811922
Domin kawo maku labarun Nigeria a lokacin da suke wakana dakare martabar arewa da Nigeria baki daya
Katsina
Gaskiya Daily Post jarida ce da zata dinga kawo muku labarai cikin harshen Hausa.
Katsina
Slm yan uwa da abokan arziki na garin yankara da kewaye anbude wannan pag ne domin tattauna matsalolin da s**ashapi yankara da kewaye dakuma bada shawara akan yadda za a magance ma...
Katsina
we are giving consultancy services on media activities and other matters arise
Kofar Kaura Katsina
Katsina
Tatauna muhamman bayanai na hon musa gafai