Accuracy News 24/7

Katsina

03/06/2023

Mai tsawatarwa Na Majalissar Dokokin Jihar Adamawa, Haruna jilantikiri, Ya Koma Tuka Keke Domin Nuna Rashin Amincewarsa Da Matakin Da Gwamnatin Tinubu Ta Dauka Na Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya.

Hoto: Amina Abdullahi Yola

03/06/2023

Yadda Wani Kwamarad Ya Tsara Harkokin Rayuwar Shi Na Yau Da Kullum Bayan Cire Tallafin Man Fetur

A matsayina na Kwamarad Zubairu Magaji Ahmad na yanke hukunci Kamar haka:

1. Duk wata tafiya da zata lashe abinda yakai N1000 NA SOKE TA. Wannan ya shafi tarurruka, daure-dauren aure, wanda ya Zama dole.

2. Duk tafiyar da Zan kashe N2000 wadda bazan samo N5000 ba na SOKE TA.

3. Tafiyar da Zan samu daidai kudin da na kashe kuwa sai nayi dogon nazari.

4. Zan kwana biyu ba'a ganni online ba, saboda cike gibin da janye tallafin man fetur ya jawo.

Wannan matsaya sai abinda Allah yayi jama'a.

Nagode
Cmrd.Zubairu Magaji Ahmad
C.E.O: ZBINMAK3 GLOBAL RESOURCES
Just for fun😂😅😅😅

02/06/2023

An Kaddamar Da Sabon Tambarin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Ta Kwararu Ta Najeriya, Tare Da Canza Sunan Gasar Daga NPFL, Zuwa ( Nigeria Premier League) Wato Firimiyar Najeria.

02/06/2023

Amarya Da Ango.

Allah Ya Bada Zaman Lafiya Da Zuri'a Dayyiba.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

Tsohan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Ya Kai Ziyara A Fadar Mai Martaba Sarkin Daura

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Ya kai ziyarar barka da juma'a a fadar mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk.

Ziyarar na da nufin mika godiya ga Mai Martaba Sarkin akan gagarumar Daba da aka shirya mashi, a lokacin da ya dawo gida bayan karewar wa'adin mulkin shi.

02/06/2023

Raɗe-raɗin Cewa Na Mallaki Naira Tiriliyan 9 Labarin Kanzon Kurege Ne - Cewar Gwamna Lawal Dauda Dare

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya musanta ikirarin da ake yi na cewa ya bayyana kadarorin da ya kai naira triliyan 9.

Gwamnan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris ya fitar a ranar Juma’a a Gusau, ya bayyana labarin a matsayin ƙage da aka shirya domin kawar da hankalin sabuwar gwamnati daga yunƙurinta na ceto Zamfara.

Ya kara da cewa wadanda s**a fadi zabe ne s**a yaɗa ƙarairayin, kamar yadda s**a yi a lokacin yaƙin neman zabe.

Sanarwar ta bayyana cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali wajen ganin ta samar da natsuwar da ake bukata a cikin harkokin mulki a jihar domin sauke nauyin alhakin da ke kan ta.

Sanarwar ta kara da cewa: “Ba za a dauke mana hankali da irin wadannan labaran na karya da ke kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu ta kuduri aniya kuma ta mayar da hankali kan kudirinta na magance matsalar tsaro da ilimi da samar da ruwan sha da inganta kiwon lafiya da noma da sauran kalubalen tattalin arziki da s**a addabi jihar.

Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyi da ayyukan da gwamna ya yi alkawrin gudanarwa.” kamar yadda sanarwar ta ce.

Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa ya ce gwamnatinsa na matukar aiki a kokarinta na cetowa da kuma sake gina jihar Zamfara, inda ta mayar da hankali wajen ganin ta cika alkawuranta.

Ya kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da ƙaryar da ake yaɗawa da gangan domin a ɓata wa sabuwar gwamnatinsa suna.

02/06/2023

Dan Majalissar Tarayya Na Mazabar Mashi Da Dutsi Da Hukumar Zabe Ta Baiwa Takardar Sheda, Nazifi MB Mashi, Ya Ziyarci Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina Na Jam'iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke.

02/06/2023

Tsadar Man Fetur A Najeriya.......

Wani Dalibin Jami'ar Maiduguri Kenan Da Ya Fara Zuwa Makaranta Akan Jakin Sa Sabili Da Tsadar Man Fetur Da Ake Fuskanta A Najeriya.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

NLC Zata Shiga Yajin Aiki Akan Cire Tallafin Man Fetur

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta shirya shiga yajin aiki na game gari bisa ga cire tallfin man fetur da gwamnatin Kasar ta yi.

Majiyar Accuracy News 24/7 ta bayyana cewa, Kungiyar zata tsunduma yajin aikin game garin ne a ranar Laraba mai zuwa, idan har Gwamnatin Tarayya bata dauki wani mataki ba akan lamarin.

Idan dai za'a iya tunawa, Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man a cikin wannan mako, kamar yadda Gwamnatin baya ta tsara.

Lamarin cire tallfin man ya haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a fadin Kasar ta Najeriya, wanda ya sanya yan Kasar cigaba da kuka akan lamarin.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

Masha Allah.

Amarya Da Ango, Allah Ya Sanya Albarka Ya Basu Zaman Lafiya.

02/06/2023

MB Mashi Ya Karbi Shedar Lashe Zabe Daga INEC Bayan Kotu Ta Kwace Daga Majigiri

Zababben Dan Majalissar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Mashi da Dutsi Honorabul Nazifi MB. Mashi, ya karbi shedar lashe zaben shi daga Hukumar Zabe Ta Kasa Mai Zaman Kanta.

Mika shedar lashe zaben ga M.B Mashi ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke inda aka amshi kujerar daga hannun Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri.

A sabili da hakan ne ya sanya Hukumar Zaben ta bi umarnin kotun kuma ta mika takardar shedar lashe zabe ga M.B Mashi.

02/06/2023

Shugaban Majalissar Dokokin Jihar Katsina Ya Zama Jakadan Zaman Lafiya Na Duniya

Wasu Kungiyoyin Kasa Da Kasa masu suna "Leeway Peace and Human Rights Foundation" da "Access To Human Rights International da "Alliance Of The People Of The World" da Cholan Book Of World Record da sauransu, sun karrama Shugaban Majalissar Dokokin Jihar Katsina Alhaji Tasi'u Musa Maigari, a matsayin Jakadan Zaman Lafiya na Duniya na shekarar 2023.

Majiyar Accuracy News 24/7 ta bayar da rohoton cewa, bikin bayar da lambobin yabon wanda ya gudana a dakin taro na Shugaban, ya samu halartar Dan Majalissa mai wakiltar Karamar Hukumar Kankia Alhaji Salisu Hamza Rimaye, da takwaran shi na Karamar Hukumar Ingawa Alhaji Abubakar Suleiman Tunas.

Mai magana da yawun Kungiyoyin ya bayyana cewa, sun yanke shawarar karrama Shugaban Majalissar ne bayan gudanar da zurfin bincike akan Shugaban Majalissar da ya fi tafiyar da harkokin shugabancin shi cikin salama a fadin Jihohin Najeriya.

A cewar shi, shugaban Majalissar ya bayar da dumbin gudummuwa ta fuskar tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin Majalissar da bangaren zartaswa na Jihar, wanda ya sanya aka cimma dumbin nasarori wajen shimfida dumbin ayyukan cigaba ga jama'ar Jihar Katsina.

Ya yi fatan cewa lambar yabon zata kara kwarin guiwa ga Shugaban Majalissar ta fuskar kara kaimi wurin kawo cigaban al'umma da Jihar Katsina baki daya.

A nashi jawabin, Shugaban Majalissar Alhaji Tasi'u Musa Maigari ya bayyana godiyar shi akan wannan karamci da Kungiyoyin s**a yi mashi.

Alhaji Tasi'u Musa Maigari ya danganta nasarorin da Majalissar ta samu bisa ga hadin kai da goyon bayan da ya samu daga yan uwanshi sauran yan majalissu, sai ya yi masu godiya akan hakan.

Daga nan sai ya bada tabbacin cewa zai kara jajircewa wurin taimakon al'umma da kuma kawo cigaban Jihar Katsina.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

Shugaba Ahmed Bola Tinubu, Ya Gana Da Gwamnonin Jam'iyyar APC A Fadar Shugaban Kasa.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

Dole Ne Ku Biya Haraji Kamar Yadda Doka Ta Tanada - Hukumar Tattara Kudin Haraji Ta Katsina Ga KEDCO Da Bankuna

Hukumar Tattara Tattara Kudin Haraji ta Jihar Katsina (KTIRS), ta gargaɗi kamfanin Rarraba Wutar Lantarki wato KEDCO, da wasu bankuna guda 3 da ke Jihar akan rashin biyan kudaden haraji ga Hukumar.

Shugaban Hukumar,Alhaji Mustapha Muhammad Suraj ne ya yi wannan gargadi bayan da ya jagoranci sauran jami'an Hukumar domin lika takardun gargadi a Bankunan da kuma Kamfanin na KEDCO.

Majiyar Accuracy News 24/7 ta bayyana cewa, bankunan da Hukumar ta yi ma gargaɗin sun haɗa da Bankin Sterling da Stanbic IBTC da kuma bankin Unity, dukkan su a cikin Birnin Katsina.

Kamar yadda Shugaban ya bayyana, an ɗauki wannan mataki ne bayan da Hukumar tashi ta yi iya bakin kokarin ta na ganin wadanda abin ya shafa sun biya harajin kamar yanda dokar Kasa ta yi tanadi.

Alhaji Mustapha Muhammad Suraj ya ce, sun ba kamfanin da bankunan makwanni biyu domin su biya kudaden da gwamnatin jiha ke bin su ko kuma Hukumar ta ɗauki matakin da doka ta yi tanadi akan lamarin.

Kamar yadda ya tabbatar, doka ta bada dama ga Hukumar akan ta tilasta wa duk wani mutum ko kamfani biyan haraji, saboda haka ba za'a zura ido ana ganin kamfanoni na bijirewa biyan harajin ba.

Daga nan sai ya tabbatar da cewa, Hukumar ba zata yi kasa a guiwa ba wurin cigaba da tabbatar da Kamfanoni da sauran masana'antu na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi.

02/06/2023

Na Ci Amanar Jam'iyyar Labour Idan Na Karbi Mukami A Gwamnatin Tinubu - Cewar Farfesa Utomi

Jigo a Jam'iyyar adawa, wato Labour Part, Farfesa Pat Utomi, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa Tinubu ya nada shi a minista a Gwamnatin shi.

Utomi ya bayyana cewa karbar mukami a gwamnatin Tinubu cin amana ne ga jam'iyyarsa ta Labour.

Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da wannan rahoto da ke ta yawo a kafar sadarwa cewa sabon Shugaban Kasar ya nada shi mukamin Minista.

Photos from Accuracy News 24/7's post 02/06/2023

AIKIN HAJJIN 2023 : Maniyyata Aikin Hajji Daga Jihar Katsina Su Sama Da 1000 Sun Isa Kasa Mai Tsarki

Daga Badaru Bello Karofi.

Jami'in Hulda Da Jama'a Na Hukumar Kyautata Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Katsina.

Sama da maniyyata aikin hajjin bana su 1000 ne yan asalin Jihar Katsina s**a isa Kasa Mai Tsarki domin gudanar da aikin hajjin na bana.

Jirgi na farko da ya yi jigilar maniyyatan ya bar Filin Sauka Da Tashin Jirage na Malam Umaru Musa Yar'adua da maniyyata 543 a ranar 31 ga Watan da muke ciki da misalin karfe 9:30 na dare, kuma ya isa filin Jirgi na Sarki Abdul'aziz lami lafiya.

Haka zalika, jirgi na biyu da ya yi jigilar maniyyatan ya tashi da mutane 527 a ranar 2 ga Watan da muke ciki, da misalin karfe 2:04 na dare kuma shima ya isa Kasa Mai Tsarki lami lafiya.

Amirul Hajji na Jiha wanda kuma shine Shugaban Majalissar Dokoki na Jihar Katsina da Shugaban Hukumar Kula Da Jin Dadin Alhazai ta Jiha Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, da sauran Mambobin Kwamitin Aikin Hajji, dukkan su sun shaida tashin maniyyatan zuwa Kasa Mai Tsarki.

Shugaban Hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, ya bayyana gamsuwa akan yadda jigilar maniyyatan ke gudana, sai ya h**e su akan su kasance masu bada goyon baya ga masu ruwa da tsaki da jami'an aikin hajjin, domin samun nasara.

02/06/2023

TA TABBATA : Femi Gbajabiamila Shine Shugaban Ma'aikata Na Fadar Shugaban Kasa

Rohotannin da ke shigo ma Accuracy News 24/7 na nuni da cewa,ta tabbata cewa Shugaban Majalisaar Wakilan Najeriya Rt.Hon. Femi Gbajabiamila shi ne Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Shugaba Tinubu ya sanar da hakan yayin taronsa da gwamnonin APC a cewar rahotan.

Tinubu ya kuma nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin Mataimakin Shugaban Ma'aikatar Fadar Shugaban Kasa.

Wane Fata Kuke Masu?.

02/06/2023

Hadejia Ya Zama Mataimakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa

Shugaban Bola Ahmed Tinubu,ya naɗa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin Mataimakin Shugaban Ma'aikatan Fadar sa.

Wane Fata Kuke Mashi?.

02/06/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Dattijo Alhaji Halle Jani Ya Rasu A Katsina

Allah Ya Yi Wa Tsohan Ɗan Majalisar Dokoki Da Ya Wakilci Karamar Hukumar Mani, Dattijo Alhaji Halle Jani Rasuwa A Daren Jiya Alhamis,

Alhaji Halle Jani Ya Rasu Bayan Ya Sha Fama Da Doguwar Jinya A Garin Funtua Ta Jihar Katsina.

Za'a Yi Jana'izarsa Bayan Kammala Sallar Juma'a A Babban Masallacin Izala Dake Kan Titin Zaria, Funtua A Jihar Katsina

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

02/06/2023

Tinubu Ya Kalubalanci Hujjojin Da Atiku Ya Gabatarwa Kotu Akan Zaben Shugaban Kasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci tulin kwafe-kwafen bayanan sakamakon zaɓen Shugaban ƙasa na 2023, waɗanda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Abubakar ya kwafo daga na’urorin BVAS daga jihohi 32 na fadin Najeriya.

Majiyar Accuracy News 24/7 , Premium Times Hausa ta bayyana cewa, Atiku ya gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke zama a Abuja kwafe-kwafen bayanan.

Haka nan ita ma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta nuna jayayya da rashin amincewa Atiku Abubakar ya gabatar wa kotu kwafen takardun a matsayin shaida.

Takardun waɗanda lodi ne mai tarin yawa, Atiku Abubakar a kwafo su ne da na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) daga jihohi 32, amma banda Kaduna, Kano, Katsina da Legas.

Tinubu wanda ya yi nasara a zaɓen 2023, ƙarƙashin APC, ya na ta gaganiya da faɗi-tashin kare kujerar sa, domin ganin kotu ba ta ƙwace ta bai wa Atiku da ya yi na biyu ba, ko kuma Peter Obi, wanda ya yi na uku.

Su biyun dai sun maka APC, Tinubu da INEC a kotu, kowanen su na iƙirarin a soke zaɓe a sake sabo, ko kuma a ba shi nasara.

Yayin da batun gabatar da shaidu ya bijiro a Kotu a ranar Laraba, lauyan Atiku Eyitayo Jegede, gabatar wa kotun da shirgin kwafe-kwafe na bayanan da ya kwafo daga INEC.

Babban Lauya (SAN) Jegede, ya roƙi kotu ta karɓi bayanan a shigar da su a matsayin shaidu a ƙarar da Atiku da PDP su ka maka INEC, Tinubu da APC a kotu.

Amma lauyan Tinubu Emmanual Ukala da Lateef Fagbemi da lauyan INEC Kemi Pinhiero, duk sun na ƙin amincewa da gabatar da kwafen takardun.

Atiku bai ma tsaya a nan ba, sai da ya gabatar da sakamakon zaɓe Jihar Abiya, Arewa maso Gabas ta Najeriya.

Ya kuma kwafo wasu takardun sakamakon zaɓe daga jihohin Bayelsa, Kaduna’ da Ogun.

01/06/2023

Jarumar Fina-Finan Kannywood Hadiza Gabon Ta Cika Shekaru 34 Da Haihuwa A Duniya.

Wane Fata Kuke Yi Mata?.

01/06/2023

Gwamna Radda Na Jihar Katsina Ya Bada Umarnin Garkame Asusun Ajiya Na Kananan Hukumomi Da Na Jihar

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da umurnin rufe dukannin asusun ajiya na Hukumomin Jihar da na Kananan Hukumomi da ke bankunan fadin Jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Mataimakin Gwamnan Jihar na Alhaji Faruq Lawal Jobe, kuma aka aike da ita ga dukkan Manajojin Bankunan da ke Jihar.

Majiyar Accuracy News 24/7 ta shaida cewa, takardar na dauke ne da kwanan wata na 29 ga watan Mayu, 2023.

Kamar yadda takardar ta bayyana, Gwamnan ya umurci bankunan akan su tsaida duk wata hada hadar kudi da kuɗaɗen dake cikin asusun bankunan Jihar, har sai wani lokaci nan gaba idan an ba su dama.

Binciken da Majiyar Accuracy News 24/7 ta gudanar ya tabbatar da cewa, tuni bankunan har sun bi umurnin kuma sun rufe duka asusun dake a bankunan nasu.

Idan za'a iya tunawa Gwamna Radda dai ya lashi takobin kawo sauye sauye da dama a Jihar, inda kuma ya roƙi al'ummar jihar su yi hakuri da matakan da Gwamnatin tashi zata dauka wurin kawo sauye-sauyen.

01/06/2023

Yan Majalissar Tarayyar Najeriya Da Ta Dattijai Zasu Karbi Kudin Sallama Sama Da Naira Biliyan 30

Hukumar Gudanarwar Majalisar Dokokin Najeriya ta shirya tsaf domin fara biyan Sanatoci da Yan Majalisar Wakilai masu barin gado kudaden sallama da s**a kai Naira biliyan 30.

Hakan dai na zuwa bayan karewar wa'adin Yan Majalissun, bayan da aka gudanar da zaben shekarar 2023.

Da dama daga cikin yan majalissun dai basu samu damar komawa Majalissar Kasar ba, sabili da shan kaye a zaben fitar da gwani ko kuma bayan zaben game gari.

Photos from Accuracy News 24/7's post 01/06/2023

Gwamnan Jihar Zamfara Dr.Dauda Lawal Dare Ya Duba Ayyukan Hanyoyu Da Wasu Ayyukan Cigaba Da Ake Aiwatarwa A Jihar.

01/06/2023

......WE NEED NEW JIGAWA STATE
....An open Letter to M. Umar Namadi, No1

By The Third Eye

When he assumed office as a sworn-in elected governor on Tuesday 30th May 2023, Malam Umar Alh Namadi had one things very clear in his mind , that , in government , there are only permanent secretaries not permanent governors.

What this means is that , unlike the permanent secretaries , the constitution stipulates a four year term and another four years for the second term . There is no third term tenure and even the second term tenure is not automatic .

Malam Namadi , a 1963, Kafin Hausa born chartered accountant , knew within him that any governor who does not take cognisance of this fact and strives to perform , will have nothing to show at the end of his first tenure , if he is looking forward to a second term mandate.

With above facts at the back of his mind , the former MMR Teachers College old boy swung into action on Wednesday 31st May 2023 with a determination to make difference of his predecessor in his first term, in order to make his second term mandate a mere formality , with the appointment of a quality and capacity Secretary to the state government , M Bala Ibrahim , Professional , highly principled and integrated accountant general Abdullah A G Shehu and matured chief of staff Sen Mustapha Makama an office that was ignored and abandoned for good eight years before his swearing -in.

However , these quick response at a right time of this former financial controller of Dangote group of companies , has to follow another action to contend with. That may be an issue of doing away with gate crushers. I mean those who are not even within the line- up of the club , but striving to get fielded as first eleven. Some of whom put every obstacle on the way of Danmodi, just to make sure he didn't succeed in his dream of becoming a governor before and during electioneering campaign .

Be warn please, (though just a Journalist) , but I am afraid such people are now under the influence of post power syndrome , and may go to any length to deceive been trusted .

01/06/2023

Lauyoyin Peter Obi Da Jam'iyyar Labour Sun Fuskanci Matsala A Kotu

Rohotannin da ke shigo mana na nuni da cewa lauyoyin Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar Labour, sun fuskanci matsala a kotu, a cigaba da sauraron karar da s**a shigar akan zaben 2023.

Hakan ya faru ne yayin da kotun ta fada musu cewa ba su shirya takurdun da s**a kawo a matsayin hujja ba, kamar yadda kotun ta umurta ba.

Hakan ya janyo kotun ta dakatar da shari'ar aka basu minti 10 don su sake shiryawa.

Photos from Accuracy News 24/7's post 01/06/2023

Subhanallah !!! - Malam Aliyu Umar Kenan Da Yan Bindiga S**a Fasa Gidan Shi S**a Yi Garkuwa Da Shi A Unguwar Mere Da Ke Cikin Garin Dandume A Jihar Katsina.

Allah Ya Kubutar Da Shi Cikin Aminci!

Daga Yellow Maishadda Funtua.

01/06/2023

Gwamnatin Tarayya Bata Da Kudin Biyan Tallafin Man Fetur - Cewar Mele Kyari

Shugaban Kamfanin Man Fetur, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da kudin cigaba da biyan tallafin mai.

Mele Kyari ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu a Abuja.

Mele Kyari ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ba ta biya tallafin mai na shekarar 2022 da 2023 ba duk da yana cikin kasafin kudi na shekarun biyun.

A cewar sa, banda rashin iya biya kudin tallafin da kamfanin ya yi, Gwamnatin Tarayya har yanzu ba ta samar da kudade na biyan tallafin ba tun farkon wannan shekara.

“Matsalar anan ita ce, kasar ba ta da kudin da za ta ci gaba da biyan tallafin. “An samar da tiriliyan 6.3 a shekarar 2022 da kuma tirilian 3.7 na shekarar 2023 har zuwa tsakiyan shekara, amma ko kwabo ba a biya ba kuma dole zamu biya haraji da sauran abubuwan da s**a zama dole saboda babu yadda zamu yi".

01/06/2023

Ban Samu Ko Sisin Kwabo Ba A Lalitar Gwamnatin Jihar Zamfara - Cewar Dauda Dare

Daga: Ibrahim Maazu Mada Bakenawa

Sabon gwamnan Jihar Zamfara Dr. Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa bai samu ko sisin kwabo ba a cikin asusun Gwamnatin Jihar, bayan da ya dafe madafun ikon mulkin Jihar.

Dr. Dauda ya faɗi hakan ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon vision FM da ke Gusau, da ta gudana a Fadar Gwamnatin Jihar.

Dr Dauda Lawal ya ce abun mamaki shine, hatta kayan gidan Gwamnatin an wawushe su, domin a cewar sabon gwamnan ko irin gas cooker,fanka,plasma ba abinda aka bari.

Sabon gwamnan ya ce amma wannan ba shi ne a gaban sa ba, babban abinda ya sa a gaba shi ne fita kunyar Zamfarawa da s**a nuna masa halacci a lokacin zabe.

Dr Dauda Lawal dare ya yi kiran Zamfarawa da su bashi cikakken haɗin kai don kai Zamfara a tudun muntsira.

©Zuma times Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Ku Shakata Da Dan Moyi, Mawakin Damben Gargajiya A Wakar Shi Ta Lawwalin Kagara.
Sakon Taya Murna Ga Zababben Gwamnan Jihar Katsina Da Mataimakin Shi Malam Dikko Ummaru Radda Da Honorabul Faruk Lawal J...
Tattaunawa Ta Musamman Da Injiniya Abubakar Shehu Kaikai, Tsohon Dan Takarar Kujerar Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar...
Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Labour Party Peter Obi,  Ya Janyewa Takwaransa Na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abub...
Ku Shakata Da Dr.Surajo Mai Asharalle, Garkuwan Dr.Mamman Shata Katsina, A Bikin Ruguntsumin Sallah Na Shekarar 2021, A ...

Telephone

Website

Address

Katsina
Other Media/News Companies in Katsina (show all)
Jaridar Gizo-Gizo Jaridar Gizo-Gizo
Shahura
Katsina

Domin samun Labarai tare da ruhotanni akan al'amuran da s**a shafi tsaro a Nijeriya tare da makwabta

DMCV Online News DMCV Online News
Lay Out
Katsina

This page is meant for local and international news

Hausa da Al'adu Hausa da Al'adu
No 140 Mani House, Yahaya Madaki Way Kofar Ƙaura New Lay-out Katsina
Katsina

Hausa da Al'adu is a platform that is being operated by CONTENT AND CLIPS Media Services Limited, a

Kukan Kurciya Daily Post. Kukan Kurciya Daily Post.
Katsina

Success through labour

Katsina Digest Katsina Digest
Katsina

Katsina Digest is a news outlet that serves as a Gateway To The Home Of Hospitality in Nigeria 🇳🇬

Arewa Daily Reporters Arewa Daily Reporters
Yahaya Madaki Way
Katsina, 811922

Domin kawo maku labarun Nigeria a lokacin da suke wakana dakare martabar arewa da Nigeria baki daya

Gaskiya Daily Post Gaskiya Daily Post
Katsina

Gaskiya Daily Post jarida ce da zata dinga kawo muku labarai cikin harshen Hausa.

Smart∆ngle Smart∆ngle
Katsina

Yakara a yau news Yakara a yau news
Katsina

Slm yan uwa da abokan arziki na garin yankara da kewaye anbude wannan pag ne domin tattauna matsalolin da s**ashapi yankara da kewaye dakuma bada shawara akan yadda za a magance ma...

Popular News Hausa Popular News Hausa
Katsina

we are giving consultancy services on media activities and other matters arise

Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai
Kofar Kaura Katsina
Katsina

Tatauna muhamman bayanai na hon musa gafai