People's Mirror
We Publish Online & Print News as well as TV & Podcast. We are committed to publishing incisive, obj
Gwamnonin Arewa maso Gabashin Najeriya, a lokacin da s**a halarci taron yankin wanda aka gudanar a jihar Adamawa ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba.
📸 - Gwamnatin jihar Gombe/Bala Mohammed/X
Daga jiya da dare zuwa yanzu, kamfanin MTN yana fuskantar matsalolin Network na tura Data da Recharge Card.
Ya Kuke ganin wannan matsalar agurinku.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ta tabbata dai cewa takardun hukuncin kotun ɗaukaka ƙara sun tabbatar da cewa Engr. Abba Kabir Yusuf ne halastaccen gwamnan jihar Kano ba Gawuna ba in ji Haruna Isa-Dederi, kwamishinan shari’a na jihar.
Mé zakú cé?
Hotunan jana’izar darakta Aminu S. Bono wanda ya rasu da yammacin jiya Litinin.
Ubangiji Allah yajikansa da sauran yan uwa?
INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN
Allah Yayiwa Shahararren Darakta a Masana’antarmu Kannywood AMINU S BONO Rasuwa.
Muna Addu’ar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Kurakuransa Yasa Aljanna Ce Makomarsa. Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani.
R.I.J.F 😭😭😭😭
YANZU - YANZU: Hukumar Hisbah Ta A Ƙarƙashin Sheikh Malam Aminu Ibrahim Zauna Da Asalin Ƴan Kannywood
Me za ku Ce?
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta ce kada fa jama'a su riƙa yi mata kallon wata uwa ko kuma babbar macce, saboda ita a halin yanzu shekarunta 28 kuma cikakkiyar budurwa ce ɗanya shakaf bata taɓa sanin ɗa namiji ba
Majiya: Hausa News Reporters
Me za ku Ce?
Hukumomin lafiya a yankin Gaza na Falasdinu da Isra'ila ta yi wa ƙawanya sun bayyana cewa, ba za a iya ƙidaya adadin wadanda s**a mutu na baya-bayan nan ba saboda katse hanyoyin sadarwa na waya da kuma intanet da Isra'ila ta yi a Gaza.
Ga yawan mace-mace da ɓarnar da Isra'ila ta jawo a yankin na Falasdinawa, bisa bayanan baya-bayan nan
Daga Abubakar Saleh
Boko Haram sun kai hari kan tawagar Motocin Gwamnan Jihar Yobe a hanyar Maiduguri!
Daga Abubakar Saleh
Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai wa ayarin motoccin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe hari kan hanyar Maiduguri - Damaturu, inda s**a kashe yan sanda biyu tare da raunata wasu biyu. DUBA Harin ya faru ne a ranar Juma'a bayan gwamnan ya halarci taron yaye dalibai karo na 24 a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno, rahoton Channels TV. A cewar wani shaidan gani da ido, wanda ke cikin ayarin motoccin amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan ta'addan sun bude wa ayarin motoccin wuta ta hannu biyu na titin, suna harin jagoran. Ya ce: "Da kyar muka tsira da ranmu yau. An kai wa ayarin motoccin hari tsakanin Beneshiekh da Mainok, kasa da kilomita shida zuwa Damaturu bayan halartar taron yaye daliban Jami'ar Maiduguri
Me za ku Ce?
Sabon Hoton Amarya Kuma Matashiyar Likita Dr. Naima Idrís Bayan Walimar Bikin Aurèn Ta
Ku sanya wa auran ta albarka.
Kotun 'Daukaka Kara ta Kori karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar da yake kalubalantar Hukuncin Kotun Tribunal data baiwa APC Nasara.
Kotun ta kuma tabbatar da Nasara ga Dakta Nasiru Yusuf Gawuna kamar yadda Kotun Farko tayi.
Me za ku ce?
CANJIN SHEƘA: Matashin Ɗan Majalisan nan da ya kada tsohon Kakakin Majalisar Dokokin jihar Yobe a zaɓen 2023 Lawan Musa Majakura, ya fice daga jam'iyyar PDP da ya samu nasara a cikinta zuwa APC.
Me za ku ce?
Saura mintuna kalilan gabanin yanke hukuncin gwamnan Kano a Kotun koli tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna.
Wakilan Jam'iyyar NNPP da na APC na jihar Kano sun hallara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.
Waye ku ke yiwa fatan Nasara?
Muhadu a comment section
Nishadi
Idan kana tunanin kana cikin tashin hankali da damuwa toh wannan mutumin yafika, Kwangila akabashi narushe wani gida saida yagama ashe nakusa dashi akace yarushe.
Matashin Dan Kasuwa Ya Rataye Kansa A Kano
Matashin dan kasuwar ya shiga damuwa bayan da wasu abokan kasuwancinsa s**a damfare shi kayan da ya saya da kudaden rance.
An tsinci gawar wani dan kasuwa mai shekaru 35 a duniya da ake zargin ya rataye kansa a wani daki da ke unguwar Sharada a Kano.
An gano gawar matashin dan kasuwar ce da wasikar da ya rubuta cewa: “A yi hakuri. Amma sauran ba sai na bayyana ba.”
Me za ku Ce?
A Najeriya Ɗan Daudun da Ya Sauya Halitta ya Koma Mace na Neman Taimako bayan Tiyatar Dashen Ɗuwawun da aka masa Ya zo da Gardama
Wani shahararren ɗan Daudu a Najeriya mai suna Hau Boogie na neman taimakon 'yan Najeriya inda ya buƙaci su tara masa kuɗi domin ceton rayuwarsa, ya ce ba ya son ya mutu.
Ɗan daudun ya shiga halin ni 'yasu ne, bayan da ya sauya halitarsa zuwa na tsaleliyar budurwa, sai dai an sami akasi ne a lokacin da aka yi masa tiyatar dashen ɗuwawu, inda aikin yazo da gardama har ta kai ga ya koma sanya pampas, yan zu haka yana roƙon 'yan Najeriya su tara masa kuɗi domin ceton lafiyarsa.
Me za ku Ce?
Kai tsaye daga kotun Majistare dake birni Lafia fadar gwamnatin jihar Nasarawa, domin fara sauraron karar da a gurfanar da mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara bisa ɓatanci ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lauyoyin bangaren da su shigar da kara sun gama kintsawa suna jiran karasowar Alkali.
Ku kasance damu domin jin yadda shari’ar zata kaya.
Gobara ta lakume wasu sassan shaguna a kasuwar Gomboru dake Birnin Maiduguri
Daga Abubakar Saleh
A safiyar yau ne muka samu labarin aukuwar gobara a kasuwar Gamboru dake nan Birnin Maiduguri inda tuni hukumar Borno State Emergency Management Agency-SEMA da ma’aikatar Ministry of Information and Internal Security, Borno State s**a tabbatar da aukuwar iftila’in.
Shin ko kun duba balance na layinku na MTN toh karku bari a barku layin MTN sun Yafewa Kowa Bashin da Yaci a Layin sa Kuyi Check Balance *310 # Yanzu... sai kubamu labari
Daga Abubakar Saleh
Me za ku Ce?
WATA SABUWA: matar da take sayar da turaren mallakar miji, auren ta ya mutu.
Fitacciyar mai sayar da maganin gyaran iyali a Jihar Kano, Zainab Alkhairi ta bayyana cewa, matar da take kawo mata tallen turaren mallakar miji yau sati 1 kenan da mutuwar aurenta. Inji Zainab Alkhairi.
Me zaku Ce.
Yanzu haka kungiyar kwadago NLC ta dakatar da ayyukanta a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, ta hana dukkannin matafiya shiga filin jirgin.
Kungiyar tana gudanar da wannan zanga-zangar ne don nuna fushi kan yadda jami'an tsaro s**a yiwa shugaban kungiyar na kasa bugun tsiya.
Me za ku ce?
Ita ce matar Tsohon Minister Musa Ƴar'adua
Ita ce Mahaifiyar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Shehu Musa Yar’adua.
Uwar tsohon shugaban ƙasar Najeriya kuma Gwamnan Katsina Mallam Umaru Musa Yar’adua
Maman Tsohon Colonel, yanzu Sanatan Katsina, Abdul’aziz Musa Yar Adua
Jikokin ta suna Auran tsofaffin Gwamnoni.
Maganar gata Kunsan Ba'a magana.
Duk wani Abu Ita yazo mata Ƙarshe fatan ta kawai cikawa Da imani.
Kun san wata mata mai gata irin nata yanzu?
Wannan Hoto da kuke kallo ba Kare bane Biredi ne.
Shin idan aka Baku za ku iya ci🙄
Wasannin da za'a fafata a yau Talata na UEFA Champions League:
...
Domin samun damar sayen Data mai sauki ku tunutubi Abubakar Saleh
Domin neman karin bayani akan sayen Datar mu Yi magana a WhatsApp ko kira👇
08109478751
HISBAH: Murja Ibrahim Kunya ta karɓi nasihar Malam Daurawa
Ta roƙi Allah ya yafe mata kura-kuran baya, za ta fara sabuwar rayuwa
Wane fata kuke mata?
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya soki Amurka bisa matakin da ta dauka a baya-bayan nan na cire kasarsa daga wata yarjejeniyar kasuwanci tare da yin gargadi game da hadarin yin kasuwanci a kasar ta gabashin Afrika.
Daga Abubakar Saleh
Me za ku Ce?
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi watsi da bukatar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas na tsagaita bude wuta a zirin Gaza, a cewar wani jami’in Falasdinu.
Jami’in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Blinken ya jaddada a yayin ganawarsa da Abbas a birnin Ramallah dake gabar yammacin kogin Jordan “hakkin Isra’ila na kare kanta da ci gaba da yakin da take yi” a Gaza.
Ziyarar Blinken a Ramallah ya dauki kimanin sa’a guda, inda ya gana da Abbas da manyan mukarrabansa inda s**a tattauna rikicin Isra’ila da Hamas.
Ya ce Blinken ya yi alkawarin matsawa Isra’ila lamba don kauce wa cutar da fararen hula da samar da amintattun hanyoyin kai agajin jin kai, amma ya ki tattauna hanyoyin tsagaita bude wuta a wannan mataki.
Daga Abubakar Saleh
Shari'ar tsakanin Gwamnan Kano Abba da Jam'iyar APC Yanzu haka Alkali ya gama sauraron ko wanne bangere ya Kuma ce za'a Sanar da ranar Yanke hukunci ta Hanyar Sanar jam'iyar NNPP da Jam'iyar APC.
Yanzu Kuma an kira shari'a tsakanin INEC da Gawuna, shari'ar da INEC ta daukaka Kara kan Hukuncin da da Kotun korafin zabe Tribunal tayi na bayyana dan takarar gwamna a APC Nasir Gawuna amatsayin Gwamnan jihar Kano.
Daga Abubakar Saleh
Wa ku ke yiwa fatan nasara
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tare da Dr. Zakir Naik a birnin tarayya Abuja.
📷 Farfesa Isa Pantami
Bala’in girgizar kasa da ya auku a kasar Nepal a ranar 3 ga wata, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 157, yayin da mutane 170 s**a jikkata.
Abubakar Saleh
UNICEF- Ta Gaza mayar da hankali kan yin rijistar haihuwa yana tauye hakkokin kananan yara da dama a Najeriya
Asusun tallafawa kananan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF ya ce, duk da cewa shirin yin rijistar haihuwa na kananan yara ya kankama a Najeriya, amma har yanzu akwai kaso mai yawa na yaran da ba a yi wa rijistar ba.
Babban jami’in asusun mai lura da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, Mr. Rahma Rihood Mohammed Farah ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani game da gangamin wayar da kai kan batun rijistar haihuwa da aka shiryawa manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki a Kano.
Daga tarayyar
Abubakar Saleh
YANZU-YANZU: Kungiyar Hamas ta bayyana cewa, ta fasa tankokin yakin Is-ra'ila 6..
Me za ku ce?
Ranar Litinin Kotun Daukaka Kara Za Ta Saurari Karar Abba
Kotun ta sanya ranar ne bayan Gwamna Abba na Jam’iyyar NNPP ya bayyana a matsayin rashin adalci, hukuncin da kotun farko ta yanke na ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
A ranar 20 ga watan Satumba, 2023, alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin mai shari Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay s**a soke nasarar Abba, bayan sun soke 165,663 daga cikin kuri’un da ya samu a matsayin ba halastattu ba.
Alkalan sun soke kuri’un ne bisa hujjar rashin kwanan wata da kuma rashin hatimin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a jikin takardun kuri’un, abin da Gwamna Abba ya kira “rashin adalci” da kuma yi wa “tsarin shari’a dibar karan mahaukaciya.”
Abubakar Saleh
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya kadu da jin labarin harin da aka kai kan jerin gwanon motocin daukar mara lafiya a wajen asibitin Al Shifa a Gaza, inda ya sabunta kiransa na dakatar da bude wuta domin jin kai.
Antonio Guterres ya ce, wajibi ne a girmama dokar kasa da kasa. Kuma dole ne a kare fararen hula da kayayyakinsu, ciki har da ma’aikatan jin kai da na jinya da kadarorinsu. Haka kuma bai dace a yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa ba.
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta tabbatar da cewa, an kai harin kan motar daukar mara lafiya, amma Hamas ce ke amfani da ita, tana mai zargin kungiyar da jigilar mayakanta da makamai a ciki.
Har ila yau, dakarun Isra’ila sun ce, an kashe mayakan Hamas dake cikin motar, amma ba tare da bayyana adadinsu ba.
Sai dai ma’aikatar lafiya ta Gaza dake karkashin Hamas, ta ce Isra’ila ta kai harin kan motocin daukar mara lafiya, wadanda ke kwashe mutanen da s**a jikkata daga arewacin Gaza da aka yi wa kawanya, inda mutane 15 s**a mutu yayin da 60 s**a jikkata.
Abubakar Saleh
Shugaban kamfanin Facebook da Mita Mark, ya sami rauni a kafarsa ta Hagu, Mark ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram da cewa, an kammala masa aikin tsagewar kashi a kafata ta Hagu.
Yanzu-Yanzu Hadakar rundanar tsaron sojoji da jami’an DSS sun bankado wani yunkurin ‘yan Boko Haram na kai farmaki a wasu sassan Kano.
Me za ku ce?
Yara da ke zirin Gaza ke nan, wadanda rikicin da ke tsakanin Palasdinu da Isra’ila ke addabarsu. Alkaluman da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar sun shaida cewa, yara sama da 3500 sun mutu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Palasdinu da Isra’ila na wannan karo. A cewar asusun kula da yara na MDD (UNICEF), yanzu haka yara kimanin miliyan daya na matukar bukatar kariya cikin gaggawa a zirin Gaza.
Daga Abubakar Saleh
Kusan mutane 40 ne s**a mutu a jihar Yobe ta Najeriya tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram s**a bude wuta kan mai uwa da wabi da tayar da nakiya a wani kauye, wanda ya kasance babban hari na farko da s**a kai jihar ta arewa maso gabashin kasar cikin watanni 18, kamar yadda rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana a ranar Laraba.
Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, ‘yan bindigan sun bude wuta kan mutanen kauye, inda s**a kashe akalla mutane 17, sannan kuma a ranar Talatar da ta gabata ne wata nakiya ta tashi, inda ta kashe akalla mutane 20 da ke dawowa daga jana’izar wadanda harin da aka kai a baya ya rutsa da su.
Daga Abubakar Saleh
Wani kirista mai shekaru 37 ya karbi Addinin musulunci ta hannun dan Sheikh Zakir Naik, Faruq Naik, a lokacin da yake gabatar da Lecture akan Musulunci da Kiristanci, yau a Jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto.
Me za ku ce?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Telephone
Website
Address
Maitama
Abuja
No. 20 P. O. W. Mafemi Crescent, Behind Chida Hotel
Abuja, 900001
The First with verifiable News, Breaking News, Exclusives, Fact Check, Investigations
Central Business District
Abuja
We Are A Digital Media Start-up Committed To The Production Of Premium Websites, World-Class Content And High-End Mobile Apps.
Abuja
Reporting about Nigerians and the colorful lives they lead; the aspects you aren't told about in the media.
Abuja
ARISE IGALA Magazine (ISSN: 2141-7423) ARISE IGALA PUBLISHING LIMITED (RC 1822199)
Ogemere Quarter Uloshi Mean Town
Abuja
Uloshi News watch media/News publisher
Gwagwgala Opposite Nepa Office Number 23
Abuja
Crowd one platform is platform where you Invest a Sentra amount of moneys and you get double of it is not less than 2 hours time
1 Ismaila Maaman, Off Jubril Aminu, Katampe Extension
Abuja, 900108
The most credible and reliable news and entertainment outlet with a focus on youth participation in
Abuja
VIBE€Z_NG is an online platform where we give you the latest in entertainment news,sports ,music etc.