Katsina State Television KTTV

The Katsina State Television KTTV is Government Own Media Station.

28/01/2024
28/01/2024

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya halarci taron Karrama Kwamishinar Sharia ta Jihar.

27/01/2024

Jawabin Gwamna Radda

Photos from Katsina State Television KTTV's post 27/01/2024

Ziyarar Gwamna Radda a Cibiyar Songhai a Jamhuriyar Benin: Neman haɗin guiwa don ci gaban cibiyar Songhai a Mairua da Dutsinma

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya fara wata ziyarar gani da ido zuwa cibiyar Songhai da ke Port-Novo, Jamhuriyar Benin a ranar Juma’a 26 ga watan Janairu, 2024. Gwamnan ya samu kyakkyawar tarba daga Farfesa Nzamujo, shugaban cibiyar da ke ta fadi tashin ganin ta samu ci gaba ta kowane bangare. Da isar Gwamna Malam Dikko Radda da mukarrabansa, an zagaya da su lungu da sako na wannan cibiya da ta kasance a sahun gaba wajen inganta aikin gona.

Cibiyar Songhai ta kasance a kan gaba wajen ƙirƙira, musamman a fannonin aikin gona da na batun inganta yankunan karkara. Gagarumar gudunmawar da wannan cibiya ta bayar ga ci gaba mai dorewa abin yabo ne da gaske.

A yayin jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana cewa an kashe makudan kudade a cibiyoyin Songhai da ke kananan hukumomin Faskari (Mairuwa) da Dutsinma a jihar Katsina a lokacin tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema. Abin takaici, an yi watsi da waɗannan cibiyoyin tun shekaru goma da s**a gabata. Don haka, makasudin ziyarar tasa shi ne nazarin yadda cibiyar ta samu nasara a Benin da kuma lalubo damar yin hadin guiwa. Ya jaddada cewa babban makasudin shi ne a farfado da cibiyar a Katsina, domin bai matasa masu kishin kasa damar cin gajiyar wannan jari mai kima.

Gwamna Radda ya himmatu wajen neman hadin guiwa da cibiyar inganta cibiyoyin da ke Katsina, da nufin amfanar al’ummar Jihar Katsina.

A karshe ya bayyana cewa gwamnatin sa ta himmatu da kwazo wajen inganta fannin noma. Burin gwamnatin jihar Katsina ya wuce tabbatar da wadatar abinci hada nufin samar da guraben ayyukan yi masu yawa ga al'ummar jihar da ke karuwa.

Tawagar Gwamna sun hada da Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina, Hon. Jabiru Tsauri; Kwamishinan noma, Farfesa Bakori; Babban makusancin Gwamna PPS, Hon. Abdullahi Turaji; Mai ba da shawara kan tattalin arziki, Hon. Khalil Nur Khalil; Darakta Janar na hukumar bunkasa zuba Jari ta Jihar Katsina Alh. Ibrahim Jikamshi; Darakta Janar na hukumar noman rani ta Katsina, Abdulkadir Nasir da sauran su.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.

27/01/2024

Isowar Gwamna Radda

27/01/2024

Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya Liyafar Cin Abinci domin Karrama Lt. Col. Professor Abubakar Surajo Imam

27/01/2024

Gwamna Dikko Umaru Radda na duba gyaran Abatuwa da Hon. Fatihu yayi a Garin Daura

27/01/2024

Gwamna Raɗɗa ya duba asibitin da FIRS ta gina a Garin Mani...

27/01/2024

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda a Karamar Hukumar Mani wajen bude Makarantar Islamiyya

27/01/2024

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda wajen bude Makarantar Islamiyya a Garin Riya na Karamar Hukumar Mani

Photos from Katsina State Television KTTV's post 27/01/2024

Milophotography 📸

150 Persons that had the opportunity to attend a One-Day Leadership Training on Ethical Standards and Etiquette in Community Development organized by Ideas and Data Global Academy under the leadership of the Katsina State Coordinator Dr.Mustapha Shehu PhD.
The SSA Student's Matters to Katsina State Governor, Comrade Muhammad Nagaske are among the Dignitaries that attended the Training.

27/01/2024

Wedding Invitation!... Wedding Invitation!!... Wedding Invitation!!!...

27/01/2024

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda na bude Makarantar Islamiyya a Ķauyen Yammama a Ķaramar Hukumar Malumfashi

27/01/2024

Hukumar Ilimin Baiɗaya ta Jihar Katsina ta ɓullo da Ɓangaren Dubawa da Tattara Mahimman Bayanai a Ƙananan Hukumomin Ilimi 34 dake Jihar...

26/01/2024

Anyi kira ga Al'ummar Musulmi dasu kasance masu neman Ilimin Addinin Islama domin ƙarin samun cigaba...

26/01/2024

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Joɓe ya halarci taron bunƙasa tattalin arziƙi a Abuja...

26/01/2024

ta samar da hanyar da Ƙaramar Hukumar Ɓaure zata dinga samun Litar Ruwa 600, 000 a cikin awanni takwas na kowace rana...

26/01/2024

Mabiya Addinin Kirista dake Katsina sun ziyarci Mai Martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman...

Photos from Katsina State Television KTTV's post 26/01/2024

Gwamnatin jihar Katsina ta hada hannu da hukumar SMEDAN don samar da bashi mai saukin biya na Naira bilyan daya (N1 Billion) don tallafar kananan 'yan kasuwar jihar Katsina

A wani muhimmin mataki da gwamnatin jihar Katsina ta dauka ta hannun hukumar bunkasa sana’o’i ta Jihar Katsina (KASEDA), ta kulla yarjejeniya da hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa SMEDAN domin bayar da bashi ko lamuni mai saukin biya na Naira biliyan daya ga kananan ‘yan kasuwa a jihar Katsina. Abin da ya banbanta wannan bashi da sauran shi ne karancin kudin ruwa na 'interest rate' na kashi 9% kawai za a caza, wanda hakan ya sa ya zama shi ne lamuni mafi sauki musamman ga masu kananan da matsakaitan masana'antu.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a hukumance a ranar Alhamis, 25 ga Janairu, 2024, a hedikwatar hukumar ta SMEDAN da ke Idu, Abuja. Wadanda aka rattaba hannu kan yarjejeniyar suna wurin sun hada da Mr Charles Odii, Darakta-Janar na SMEDAN, da Mrs Aisha Aminu, Darakta Janar ta hukumar bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu ta jihar Katsina.

Shirin Matching Fund Programme, wani shiri ne na haɗin guiwa tsakanin Hukumar SMEDAN da Gwamnatin Jihar Katsina wanda zai ba da tallafin lamuni ga ƙananan masana'antu a Jihar Katsina bashin kudi mai tsoka. Gwamnatin Jihar Katsina da Hukumar SMEDAN kowannen su zasu bada Naira miliyan dari biyar (N500,000,000). Don fara rubu'in farko na shekarar 2024, inda za a fara bada bashin kudi N250m ga masu kananan sana'o'i.

Gwamna Radda, a lokacin da ya yi jawabai masu ma’ana, ya bayyana irin jajircewar da gwamnatinsa ke yi na inganta ci gaban kasa ta hanyar samar da ci gaban kananan ‘yan kasuwa da hanyar inganta harkokin kudi.

Gwamna Dikko Radda ya jaddada muhimmiyar gudunmuwar da kananan da matsakaitan masana'antu ke bayarwa wajen ci gaban kasa da kuma matsayinsu na masu shiga tsakani a ajandar tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya kuma bayyana irin namijin kokarin da hukumar bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu ta jihar Katsina ke yi, ya kuma jaddada muhimmancin hada hannu da hukumar SMEDAN wajen samar da ayyukan yi da kuma farfado da tattalin arziki.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Shugaban Hulumar ta SMEDAN, Mr Odii ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Radda, wanda a baya ya taba rike mukamin Shugaban hukumar na tsawon shekaru shida kafin ya hau kujerar Gwamna. Ya amince da ra’ayinsu na samar da ci gaban kasa ta hanyar bunkasa kanana da matsakaitan masana'antu tare da amincewa da kananan ‘yan kasuwa a matsayin ginshikin tattalin arzikin kasar.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.

Photos from Katsina State Television KTTV's post 25/01/2024

Gwamna Radda ya ziyarci hukumar sadarwa ta kasa NCC, domin neman hadin guiwa wajen bunkasa fasahar zamani ta ICT a jihar Katsina

Mai Girma Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya kai ziyarar aiki a hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, inda ya samu kyakkyawar tarba daga mataimakin shugaban hukumar, Dakta Aminu Wada Maida da wasu manyan jami’an gudanarwa na hukumar.

Gwamna Radda ya nuna jin dadinsa da irin kyakkyawar tarba da aka yi masa, ya kuma bayyana cewa ziyarar tasa na da nufin ba da sanayya da kuma neman hadin guiwa da hukumar don inganta harkar sadarwar zamani ta ICT a jihar Katsina.

Gwamna Radda, a yayin ziyarar tasa, ya taya Dr. Maida murnar nadin da shugaba Ahmed Tinubu ya yi masa. Ya kuma jaddada bukatar Dokta Maida ya ba marada kunya ta yadda za a kara tabbatar da cewa Katsinawa na da kishi da rike amana.

Da yake karin haske kan mahimmancin fannin sadarwa, Gwamna Radda ya bayyana cewa yana taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da tsarin tattalin arzikin musamman na zamani da Gwamnatin tarayya ta saka a gaba. Yana aiki a matsayin ginshiƙi mai muhimmanci, yana habbaka tattalin arzikin da ake buƙata, musamman wajen tallafa wa ayyukan kanana da matsakaitan masana'antu a faɗin Nijeriya har ma da makwabta.

Malam Dikko Radda ya bukaci hukumar ta bayar da goyon baya mai ma’ana wajen inganta harkokin sadarwa da na intanet a fadin ma’aikatu sassa da hukumomi a jihar Katsina, da nufin samar da ingantaccen aikin gwamnati.

Da cikakken kwarin guiwa, Gwamna Radda ya ba da tabbacin yin hadin gwiwa da hukumar da duk masu ruwa da tsaki a harkar, da nufin saukakawa da fadada ayyukan masu layukan sadarwa zuwa yankunan karkara don a samu saukin isar da sako cikin kankanin lokaci.

Da yake mayar da jawabi, Dr. Wada Maida ya nuna jin dadinsa da irin kyakkyawan hangen nesa da jagoranci na Gwamna Radda. Ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa hukumar ta ba da cikakken goyon baya ga kokarinsa tare da yin alkawarin samar da karin ayyuka domin amfanar Katsina.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media to Katsina State Governor.

Photos from Katsina State Television KTTV's post 25/01/2024

Governor Dr. Dikko Umaru Radda attended the Opening Session of the Two-Day Roundtable on Insecurity in Northern Nigeria themed: “Multidimensional Approach To Tackling Insecurity in Northern Nigeria” organized by the Coalitions of Northern Groups at Army Resource Center, Asokoro, Abuja.

24/01/2024

Wasu al'ummomomi dake a Karamar Hukumar Faskari dake Jihar Katsina sunyi kira ga Gwamnati data gyara masu gada data lalace sama da Shekara Ɗaya...

24/01/2024

Gwamnatin Jihar Katsina ta raba kayayyakin kula da kiwon lafiya a Jihar...

23/01/2024

MU YI AMFANI DA WANNAN DAMAR ZA TA YI MANA AMFANI

Baze University, Abuja a ƙarƙashin ɗaukar nauyin Babban Bankin Duniya (World Bank) sun shirya koyar da mutane kwasa-kwasai (Online Diploma Courses) kyauta ga ƴan Nigeria, amma sai da dama irin wannan damar duk ƴan Arewa ake bari a baya.

Don haka, duk mai sha'awa ya shiga ya cike, amma Courses ɗin sun shafi: Artificial Intelligence, Cyber Security, Blockchain Technology, Data Analysis, Business Intelligence, Digital Literacy, etc.

Domin rijista a shiga nan: www.ideas.bazeuniversity.edu.ng/our-programs

Allah ya bada sa’a, Ameen.
SANARWA DAGA MATAIMAKI NA MUSAMMAN GA GWAMNAN JIHAR KATSINA AKAN HARKOKIN ƊALIBAI.
Hon. Mohammed Nagaske.

23/01/2024

Rahoto na musamman akan yadda Gwamnatin Jihar Katsina zata tura Ɗalibai Karatu Ƙasashen Waje.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Gwamnan Jihar Katsina,  Malam Dikko Umar Radda ya halarci taron Karrama Kwamishinar Sharia ta Jihar.
Jawabin Gwamna Radda
Isowar Gwamna Radda
Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya Liyafar Cin Abinci domin Karrama Lt. Col. Professor Abubakar Surajo Imam
Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya Liyafar Cin Abinci domin Karrama Lt. Col. Professor Abubakar Surajo Imam
Gwamna Dikko Umaru Radda na duba gyaran Abatuwa da Hon. Fatihu yayi a Garin Daura
Gwamna Raɗɗa ya duba asibitin da FIRS ta gina a Garin Mani...
Gwamnan Jihar Katsina,  Malam Dikko Umar Radda a Karamar Hukumar Mani wajen bude Makarantar Islamiyya
Gwamnan Jihar Katsina,  Malam Dikko Umar Radda wajen bude Makarantar Islamiyya a Garin Riya na Karamar Hukumar Mani

Telephone

Website

Address


Along Batsari Road
Katsina
820101
Other Media/News Companies in Katsina (show all)
Jaridar Gizo-Gizo Jaridar Gizo-Gizo
Shahura
Katsina

Domin samun Labarai tare da ruhotanni akan al'amuran da s**a shafi tsaro a Nijeriya tare da makwabta

DMCV Online News DMCV Online News
Lay Out
Katsina

This page is meant for local and international news

Hausa da Al'adu Hausa da Al'adu
No 140 Mani House, Yahaya Madaki Way Kofar Ƙaura New Lay-out Katsina
Katsina

Hausa da Al'adu is a platform that is being operated by CONTENT AND CLIPS Media Services Limited, a

Kukan Kurciya Daily Post. Kukan Kurciya Daily Post.
Katsina

Success through labour

Katsina Digest Katsina Digest
Katsina

Katsina Digest is a news outlet that serves as a Gateway To The Home Of Hospitality in Nigeria 🇳🇬

Arewa Daily Reporters Arewa Daily Reporters
Yahaya Madaki Way
Katsina, 811922

Domin kawo maku labarun Nigeria a lokacin da suke wakana dakare martabar arewa da Nigeria baki daya

Gaskiya Daily Post Gaskiya Daily Post
Katsina

Gaskiya Daily Post jarida ce da zata dinga kawo muku labarai cikin harshen Hausa.

Smart∆ngle Smart∆ngle
Katsina

Yakara a yau news Yakara a yau news
Katsina

Slm yan uwa da abokan arziki na garin yankara da kewaye anbude wannan pag ne domin tattauna matsalolin da s**ashapi yankara da kewaye dakuma bada shawara akan yadda za a magance ma...

Popular News Hausa Popular News Hausa
Katsina

we are giving consultancy services on media activities and other matters arise

Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai
Kofar Kaura Katsina
Katsina

Tatauna muhamman bayanai na hon musa gafai